Muhimmancin Ilimi

Ilimi shi ke daga gidan da ba shi da ginshiki. Jahilci ke rusa gidan da ke da daukaka da daraja. Mu yi karatu domin zaman Duniya da Lahira

Koyi a wurin gwanaye!

Gwanancewa a cikin al’amari ita ce hanyar da zata mayar da kai kwararre, karatu a wurin gogaggun masana, na taimakawa wurin rabuwa da rudu

Zabi Wurin Darasi

Ba dole sai ka dauki kwas duka ba, kana da dama zabar darasin da kake bukata a wannan makaranta.

Siyan darasi kai tsaye

Ba sai ka je banki domin siyan darasi a wannan makaranta ba, kana da damar yin amfani da hanyoyin biyan kudi ta intanet.

Kayan karatu ba adadi

Lallai zaka samu kayan da kake bukata domin yin karatu a wannan makaranta ba tare da samun cikas ko matsala ba.

Taimako awowi 24

Idan kana da matsala zamu iya sauraren koke-koke da korafe-korafe a cikin kowane lokaci, ba Juma’a bare Lahadi.

Yin Shafukan Intanet da HTML da CSS

Wadannan hanyoyi guda biyu sune hanyar da mutum zai san yadda ake kirkiran shafukan Intanet ta amfani da tsarin da ya dace wato HTML (Hypertext Markup Language) da kuma CSS (Cascading Style Sheet).

web_design_services
graphic-tools

Ko yi Graphics da Multimedia

Duk da cewar darasi ne mai tsawo da kuma bukatar kwamfuta mai babban zubi, amma wannan kwas yana da muhimmancin ga mutumin da yake son ya san yadda ake sarrafa hotuna da bidiyo da kuma sauti kama da hada hoto da sauti ko kuma motsa zane kamar yin cartoon da makamantansu

Abin lura tare da mu

Gogaggun Malamai

Kasancewar malamai da suke karantar da darussa a wannan makaranta malamai ne gogaggu a fannoni kuma sun shahara a bangarorinsu. Tsawon shakarun da suka dauka suka karantarwa a fannonin ilimi ya sanya hankali kwanciya da su.

Darasi bayan darasi

Tsarin karanta a wannan makaranta tsari ne na bai daya, ta yadda dalibi na bukatar ya san darussan da suke gabanshi da wadanda suka ya riga ya gama. Mun tsara darussa bayan darussa domin jin dadin masu son yin karatu a wannan makaranta.

Rubutattun Darussa

Dukkan wani darasi da mutum zai dauka yana da damar yin amfani da rubutu zalla ko kuma ya yi amfani da sauti ko kuma ya yi amfani da hotuna masu mosti. 

Bayanai dalla-dalla

Dukkan wani darasi da muka dauka mun yi bayanai masu gamsarwa, kuma a cikin hanyar karantarwa mai sauki. Wannan ya sanya karatun da muke koyarwa muka yi su dalla-dalla.

Zabin karatu ko kwas

Duk da cewar akwai kwasa-kwasai manya masu daukan lokaci mai tsawo kafin mutum ya gama, a gefe guda kuma, muna da tsarin da zai baiwa mutum damar ya dauki kwas karami wanda a karshe zai bashi dagamar yin karatu a duk yanayin da zai mashi dadi.

Yin karatu lokacin da ka dama

Duk da cewar muna da tsarin lura da yadda dalibi zai yi karatu ta hanyar lura da yadda yake shiga aji da lokacin da zai amsa tambayoyi na test, ko jarabawa, mun saukaka muku mutuka domin zabin lokacin da mutum zai yi karatu.

Malaman mu

Salisu Hassan

Malami

Malami ne a Duniyar Computer.

Amina K. Muhammad

Guest Lecturer - Design

Malama ce a Duniyar Computer.

Aminu Salihu Husaini

LECTURER - ECONOMICS

Malami a Duniyar Computer

Salisu Yusuf

Malami - Computer Operation

Malami a Duniyar Computer

Our Partners

Adobe_Systems_logo_and_wordmark.svg
microsoftlogo
cinema_4d_r13_r14_logo_by_dracu_teufel666-d5nooof
w3c-logo